<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>264</hymn_number>
<title>Zo, Mu Ba da Shaida, Duniya Duk Ta Ji LW264</title>
<lyrics>[V1]
 1) Zo, mu ba da shaida, duniya duk ta ji,
 Babu damar hutu, babu damar ƙi.
 Cewar Almasihu, duk su duba ni,
 Haka za su sami rai.

[V2]
 Duniya duk ta ji, duniya duk ta ji,
 Duniya duk ta ji labarin fansarta.
 Babu damar zama, Yesu ba ma ƙi,
 Zo, mu ba da shaidarmu.

[V3]
 2) Zo, mu kafa tuta, yaƙi za mu yi,
 Yaƙin Almasihu, ba mai damar ƙi.
 Fizgi bayin duhu daga zunubi,
 Kai su wurin Sarkinmu,

[V4]
 Duniya duk ta ji, duniya duk ta ji,
 Duniya duk ta ji labarin fansarta.
 Babu damar zama, Yesu mu ke bi,
 Zo, mu kafa tutarmu.

[V5]
 3) Zo, mu faɗi laifi, roƙi gafara,
 Mu mun yi son zuciya, mu nun yi ƙyuya.
 Domin rashin ƙauna, domin ba aniya,
 Duniya tana mutuwa.

[V6]
 Yaushe za ta ji? Yaushe za ta ji?
 Yaushe za ta ji labarin fansarta?
 Yesu AImasihu, gyarta halinmu,
 Muna faɗin laifinmu.</lyrics>
</song>